Ummi Rahab
Quick Facts
Biography
Rahab Salim wacce aka fi sani da Ummi Rahab ko Ummi Takwara (an haifeta a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004) a garin Kaduna. Ƴar wasan kwaikwayo ce a masana'antar fim ta Kannywood 'yar rawa kuma 'yar talla wacce ta auri Jarumi, Furodusa kuma mawakin Hausa, Lilin Baba.
Farkon Rayuwa
An haifi Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004 a cikin garin Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.
Karatu
Ummi rahab tayi karatun firamare da sakandire a jihar Kaduna, kafin daga baya ta koma garin Kano domin ci gaba da rayuwar ta.
Sana'a
Ummi Rahab na daga cikin jaruman Kannywood da suka fara taka rawa a wasan kwaikwayo tun suna ƙanana. Ummi Rahab ta fara fitowa a fim tun lokacin tana makarantar firmare, acikin fim din da tayi fice da shi wato "Takwara Ummi". A lokacin tana da shekaru goma a duniya inda ta fito a matsayin diyar Adam A Zango. Ummi Rahab tayi fice a masana'antar fim na Kannywood kuma ta fito a bidiyon waƙoƙin Hausa da dama da suka hada da: Meleri - WUFF Dake.
Iyali
Ranar 18 ga watan yuni, 2022 Ummi Rahab ta auri Lilin Baba.
Mahadar shafukan waje
Manazarta
- ↑ "Ummi Rahab Kannywood Biography, Age, Photos, Phone Number &Net Worth - ArewAngle". 18 January 2022. Retrieved 4 October 2022.
- ↑ ttps://www.northernwiki.com.ng/cikakken-tarihin-ummi-rahab/
- ↑ Hausaflix (18 March 2022). "Tarihin Rayuwar Ummi Rahab: Tarihi cikakke, rayuwar ta a Kannywood". Hausaflix. Retrieved 4 October 2022.
- ↑ Admin (13 March 2022). "CIKAKKEN TARIHIN UMMI RAHAB - Northernwiki Jaruman kannywood". Northernwiki. Retrieved 4 October 2022.
- ↑ Hausaflix (18 March 2022). "Tarihin Rayuwar Ummi Rahab: Tarihi cikakke, rayuwar ta a Kannywood". Hausaflix. Retrieved 4 October 2022.
- ↑ https://hausa.legit.ng/kannywood/1475147-aure-ya-kullu-bidiyo-da-hotunan-auren-lilin-baba-dakyakkyawar- amaryarsa-ummi-rahab/