Nasiru Mato
Quick Facts
Biography
Alhaji Nasiru Mato (an haife shi ranar 3 ga watan Yuli, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da Uku 1973A.c) a garin Potiskum na Jihar Yobe. A halin yanzu shi ne zaɓaɓɓen ciyaman na kasuwar Potiskum kuma shugaban ciyamomin 'ƴan kasuwa na Ƙananan Hukumomin Jihar Yobe guda goma sha bakwai 17 tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu, sannan ɗan kasuwa ne yana da kamfanin furnitures mai suna 'Mato Multi Links'dake cikin garin Potiskum.
A baya ya riƙe muƙamin shugabanc
in masu sana'ar katako tun daga 2008-2018, ya zama mai ba wa ƙungiyar 'yan kasuwa "ta United Maketers Association Potiskum (UMA" O) shawara na tsawon lokaci, kana ya zama mataimakin shugaban kasuwar Potiskum (UMAPO) daga 2016-2018, ya zama shugaban riƙon kwarya na (UMAPO) daga 2018-2020.
Farkon rayuwa da Karatu
An haife shi a 03-07-1973 a cikin garin Potiskum jihar Yobe.
Dangi
Alhaji Tijjani Mato (Walin fika) Hajiya Hafsat Mato (Magatakardar Jami'ar Jihar (YSU). Mai shari'a Sani Mato, tsohon alkalin alkalan Jihar Kano.
Karatu
Damboa Primary School Potiskum, Govt day Secondary School Potiskum, Ramat Polytechnic Borno, a yanzu haka yana karatu a Jami'ar Maiduguri (UNIMAID).
Iyali
Yana da Mata biyu da 'ƴa' ƴa goma sha biyar, 15 Maza, 4 Mata 11.
Kasuwanci
Yana da kamfanin furnitures mai suna 'Mato Multi Links'.
Mukami
Shi ne shugaban kungiyar (UMAPO) ya zama mai ba wa ƙungiyar'yan kasuwa ta "United Maketers Association (UMAPO)" shawara na tsawon lokaci, kana ya zama mataimakin shugaban kasuwar Potiskum (UMAPO) daga 2016-2018, ya zama shugaban riƙon kwarya na (UMAPO) daga 2018-2020. Haka zalika, ya taba rike shugaban kungiyar yan katako na tsawon shekaru goma.
Nasarori/Kambu
Alhaji Nasiru Mato ya samu jerin lambobin yabo da kambun karramawa daga kungiyoyin da suka hada da:
- Ƙungiyar ɗalibai ta Arewa Maso Gabas (NESAN) ta karrama shi da Award.
- Kungiyar "Democratic Youth Assembly of Nigeria (DYAN)".
- "Youth Development student Association (YDSA)" sun ba shi "stake Holder" .
- "Peace Association Of Nigeria (PUYAN)".
- "Yobe South Development Organization (YOSDO) award of excellent" .
- "Youth Crisis Awareness and peace forum (YCAPF) Best Umapo chairman" .
- "Youth Initiative for Sustainable Development (YISD) icon of business development" .
- "Potiskum Main Market Youth Forum (PMMYF) Best Performing Chairman" .
- "Narto Media Team. Award of Excellence" .
- "United Market Association (ASYZ)" .