Saude Abdullahi - Aliyu
Quick Facts
Biography
Saude Abdullahi-Aliyu (an haife ta a shekara ta alif dari tara da hamsin da biyu 1952), ta fito daga gidanmasarautarWudil, ma'aikaciyar fannin ilimi na boko da na addinin Islama ce, wacce ta fara zama mace ta farko daga Jihar Kano da ta rike shugabancin makarantar Gwamnatin tarayya kuma ta rike Darakta a Ma'aikatar ilimi ta Gwamnatin tarayya, ta kasance mace ta farko da ta samu digiri daga Karamar Hukumar Wudil.
Tarihi
Saude Abdullahi - Aliyu yar asalin Jihar Kano ce, da aka haifa ranar 25 ga watan Satumban shekara ta alif dari tara da hamsin da biyu 1952, mahaifin ta mai suna Abdullahi- Maikano Mahmoud ya kasance mai rike da sarautar gargajiya ta Sarkin Fulani dagacin Tsibiri a Karamar Hukumar Wudil, Kakanta sunansa Shaykh al Islam Mahmoud, Kakan-Kakanta mai suna Dawaki Bello ya rike sarautar Sarkin Wudil, wanda yake bafulatani ne da ya taho daga Gidan Shehu Dan fodio a Kasar Sokoto zuwa Wudil ya zauna a garin Ginsau a wajen Wudil, Kafin ya shigo cikin garin Wudil tunda daga gidan Shehu Dan Fodio ya zo ana saka zuriarsa a matsayin Fulani Torankawa,sunan Mahaifiyarta Hajiya Rabi bint Shehu-Usman ibn Abdussalam(Inna) jikar Alkalin Gano mai suna Alkali Isiyaka ta wajen mahaifiyarta mai suna Hama a garin Gano na Karamar Hukumar Dawakin Kudu.
Ilimi
Ta samu shedar takardar Grade II Teachers Certificate daga Women Teachers College Kano, Nigeria Certificate in Education (NCE) English / Islamic Studies daga makarantar Advanced Teachers College, Institute of Education, Jami'ar Ahmadu Bello da takardar digiri ta Bachelors of Arts English/Islamic Studies daga Jami'ar Bayero.
Aiki
Ta fara aiki a Dorayi Primary School da Kwalli Primary School daga shekara ta, 1971 da kuma shekara ta, alif dari tara da saba'in da biyu 1972, ta yi aiki a Kano Local Education Authority a matsayin malamar makaranta ta Grade II daga shekara ta, alif dari tara da saba'in da uku 1973 zuwa shekara ta,alif dari tara da saba'in da tara1979, a makarantun Shekara Boarding Primary School, Wudil Primary School da Magwan Primary School, ta yi aikin bautar kasa National Youth Service Corps daga shekara ta,alif dari tara da saba'in da tara1979 zuwa alif dari tara da tamanin 1980, a Women Teachers College Kano, ta yi aiki a Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano daga shekara ta, 1984 zuwa shekara ta, 1995,amakarantun Women Arabic Teachers College Goron Dutse da Government Senior Secondary School Gwammaja II, ta rike matsayin Senior Mistress a Government Girls College Dala, Vice Principal a Women Arabic Teachers College Goron Dutse da Principal Shekara Government Girls Secondary School, a ma'aikatar ilimin gwamnatin tarayya ta yi aiki daga shekara ta, alif dari tara da casa'in da biyar 1995 zuwa shekara ta, 2014, ta rike Principal a Federal Government Girls College Kazaure, Federal Government Girls College Minjibir, Inspector of English Language Federal Inspectorate Service Kano, Co-ordinating Inspector Federal Inspectorate Service Kano, Principal Federal Government Girls College Potiskum, Principal Federal Government College Kiyawa, Director of Education Federal Ministry of Education.
Aure
Ta auri Alhaji Abdullahi Aliyu Sumaila a shekara ta alif dari tara da saba'in da uku1973, auren ya samu albarkar yara guda bakawai.
Manazarta
- ↑ Sumaila, Ahmed (2014). The making of a Principal: Saude Abdullahi. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
- ↑ Sadi, Badamasi (1980). Sarkin Fulani Abdullahi Maikano. Kano: Cipsco Press.
- ↑ Sumaila, Ahmed (2007). Usman dan Fodio. Kano: Aurora Kano.
- ↑ Annual Volumes of the laws of Kano State. Government Printer. 1987.
- ↑ Abubakar, Aliyu (2005). The Torankawa Danfodio Family. Kano,Nigeria: Fero Publishers.
- ↑ Ibrahim, Muhammad (1987). The Hausa-Fulani Arabs: A Case Study of the Genealogy of Usman Danfodio. Kadawa Press.
- ↑ Ibrahim, Muhammad (1987). The Hausa-Fulani Arabs: A Case Study of the Genealogy of Usman Danfodio. Kadawa Press.
- ↑ Adnanu, Sammani (2003). Wudil Local Government Graduates. Kano: Cipsco Press.
- ↑ Annual Volumes of the laws of Kano State. Government Printer. 1995.
- ↑ Babangida, Asmau (2015). Kano Female Educationist. Kano: Kadawa Gaskiya Press.
- ↑ Adamu, Saidu (2001). Women Education in Kano State. Kano: Sabon Titi Press.
- ↑ Yahaya, Bala (2005). Access to Education and Social Justice: A case study of Kano State. Kano: Sanda Press.
- ↑ Muhammadu, Baba (2018). Women's Access to Higher Education in Nigeria: A case study of Kano State. Kano: Cipsco Press.
- ↑ Kabiru, Binta (2013). Education and Kano Women. Kano: Ferota Press.
- ↑ Shazalli, Santali (2003). The Torankawa of Wudil. Kano: Kadawa Gaskiya Press.