Mustapha Ado Muhammad
Quick Facts
Biography
Alhaji Mustapha Ado Muhammad (An haifeshi ranar 27 ga watan Yuli, 1958) ɗan kasuwa ne ɗan Najeriya kuma ɗan agaji. Shi ne wanda ya kafa kuma shugaban kamfanin Ammasco International Limited, kamfanin haɗa man shafawa na farko a Arewacin Najeriya kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da man shafawa a Najeriya.
Farkon Rayuwa da Ilimi
An haifi Mustapha Ado Muhammad a Katsina a ranar 27 ga watanYuli, 1958.
Ya fara karatunsa na firamare a Gobirawa Primary School, Kano, kuma ya kammala a shekarar 1977. Ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati, Gwale, Kano, ya kamala a shekarar 1982. Bayan haka, ya samu gurbin shiga Makarantar Koyon Gudanarwa da ke Kano State Polytechnic inda ya karanta (Accounting) inda ya samu Diploma na kasa da Difloma ta Kasa a 1985 da 1989 bi da bi.
Ayyuka da muƙamai
Shugaban LUPAN
Shi ne shugaban ƙungiyar masu samar da man shafawa ta Najeriya (LUPAN).
Mamba
A watan Mayun 2017, an naɗa shi mamba a Majalisar Bayar da Shawarar Manufofin Masana’antu da Gasa ta Najeriya, Majalisar wakilai 36, ƙarƙashin jagorancin Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Najeriya.
Lambar yabo
A ranar 16 ga Oktoba, 2021, ya sami lambar yabo ta The Sun Newspaper (Industrialist of the Year Award) saboda gudummawar da ya bayar wajen bunƙasar tattalin arziki a Najeriya.
Manazarta
- ↑ Ajakaiye, Adeola (2020-12-09). "SON's DG visits Ammasco manufacturing plants in Kano". Businessday NG. Retrieved 2022-11-10.
- ↑ "The Sun Award winners 2020: Mustapha Ado Muhammad: Industrialist of our time". The Sun (in Turanci). 2022-10-02. Retrieved 2022-11-06.
- ↑ "Oil Firm to Empower 3,000 Technicians – THISDAYLIVE". THISDAYLIVE – Truth and Reason. 2020-09-15. Retrieved 2022-11-10.
- ↑ "LUPAN Partners SON Against Fake, Substandard Lubricants". Leadership News. 2022-10-06. Retrieved 2022-11-10.
- ↑ Times, Premium (2017-05-30). "Osinbajo gives Dangote, Peterside, 34 others new appointments -- FULL LIST". Premium Times Nigeria. Retrieved 2022-11-10.
- ↑ "The Sun award priceless honour –Mustapha Ado Mohammed". The Sun Nigeria. 2021-10-04. Retrieved 2022-11-10.