Mr442
Quick Facts
Biography
Mubarak Abdulkarim Wanda aka fi sani da Mr 442 An haifeshi a cikin garin Zaria jihar Kaduna 13-9-1995.
KARATU
yayi karatun Firamare da sakandiren sa a Cikin garin zaria sannan Ya karanci ilimin halayyar dan adam (Sociology) a jami'ar Amurka ta Addinai a jamhuriyar Benin republic.
SHAHARA
Yafara Shahara ne lokacin da ya saki wakar sa da yayi akan wani Sanata mai taken jarumar masana'antar Kannywood Maryam booth Mai taken Zindir. Mr 442 ya cigaba da yin sunane a cikin kasa Najeriya da Nijer bayan cigaba yin wakoki masu jawo cece kuce a cikin Al'umma, inda ake Alakanta wakokin nasa da Wakokin Batsa wanda hakan Ya saba da Al'adar Hausawa. Inda shi kuma yake kare kansa da cewa jama'a ne suke masa fahimtar da ba dai-dai ba, Shi yanayi hakane Domin janyo Hankalin mutane Su fahimci sakon dake cikin Wakokinsa.
Mr442 da Safaa
Haduwar 442 da Safiyya Yusuf Wacce aka fi sani da Safaa Safaa Tayi tasiri matuka Wajen Kara fito da shaharar 442 a idon duniya Bayan Sun saki wakarsu ta farko mai Taken Kwalele tare da Gudunmawar Madox Tbb sannan wakoki kamar su inda ass, tabarah, a abuja, tunkwal da dai sauransu. Amma daga baya ta ci amanar sa saboda an kama shi a kasar nijar amma bayan fitowarsa yazo ya fita daukaka nesa ba kusa bah.
WAKOKIN MR 442 KAFIN A KAMA SHI A NIJAR
A halin yanzu dai yayi wakoki sama da 500 Kadan daga cikin wakokin sa:
- Zindir
- Ajino Moto
- Soro soke
- Burauba
- daka
- Sai Monday
- Kwalele ft Safaa, Madox Tbb
- Mace
- Dan hisba leaked
- Bata kwana
- Sai babanshi ft tapshak
- Package ft King Sammy
- Shagali
- Yin shine
- Akan ki
- Yan mata
- Corona
- Bamaji ft Teeswags
- 2-0 ft tee r
- Zarians ft tee r
- Jikinta ft Ovista, Teeswagg, and Tee R
- Tabalaga ft Teeswags
- Siki saka
- Kanawan mene
- Dalla Dalla
- Lokaci
- Kotu
- Mace
- Riga
- jigida
- Yaga mehn ft murja
- Tunkwal ft Safaa, murja
- Basu wuta Ft Safaa
Da sauran su.
BAYAN FITOWAR SA DAGA GIDAN YARI
Bayan an sake shi yayi wakoki kamar haka:
- Sai ya faru
- Li-ela-fiy
- Zasu sha mamaki
- Sakon ku
- Chan musu
- Kashe kudi ft. Ovizta
- Growth (daukaka)
- Our father (baban mu)
- Bariki ft. Rumerh
- Culture (al'ada)
- Radadi
- Tana sona
- Kano ft. Ngulde
- Money movement ft. Zinoloesky
- Trending ft. King kabeer , Aliboss
- Tasanu
- Paris (a kasar france)
- Arewa international anthem (a kasar france)
DA DAI SAURANSU