peoplepill id: khuraira-musa
KM
Nigeria
1 views today
1 views this week
The basics

Quick Facts

Places
Work field
Gender
Female
Place of birth
Lere, Nigeria
The details (from wikipedia)

Biography

Khuraira Musa yar'Najeriya ce, mazauniyar Amurka, ta kasance shahararriyar kuma kwararriyar mai-kwalliya ce, shafe-shafe da kuma taimakon alumma, itace wacce ta samar kuma shugaba ce ta kamfanin Khuraira Cosmetics. Khuraira ta shahara a fagen kwalliya da shafe-shafe na duniya, wanda ta kasance tana gudanar da ajujuwan koyarwa ga mutane daga duniya baki daya. A rayuwar ta tayi kwalliya ga shahararrun mutane kamar su, Brandy, Mandy Moore, Paula Abdul, Kirstie Alley, Natalie Cole, Cher, Suzanne Douglas, Trista Rehnda kuma Dr. Suzanne Rice.

Farkon rayuwa da aiki

Khuraira Musa an haife ta a Ƙaramar hukumarLere Jihar Kaduna, Najeriya. Ta rasa mahaifiyar ta a lokacin haihuwar ta, wanda hakan ne yasa ta rayu a gidan rainon marayu dake yankin Rukuba/Bassa a Jihar Plateau, amma bayan nan ta koma jihar Kaduna har sai da ta kammala makarantar sakandare. A 1992 taje kwaleji a Tarayyar Amurka wanda anan ne ta fara aiki a shaguna.

Aikin agaji

Khuraira Musa ta kafa gidauniyar da ake kira da suna Arewa Development Support Initiative (ADSI) hukuma wacce bata gwamnati ba, da niyyar taimakawa cigaban matasa da mata a yankin Arewacin Najeriya. Gidauniyar na tallafawa da samun karatu ga mata, sana'o'in hannu da dabarun kasuwanci. Khuraira itace ta samar da makarantar Zainab Memorial saboda karantar da marasa karfi musamman marayu waɗanda ke a Bassa/Rukuba a Jihar Plateau.

Manazarta

  1. Khuraira Cosmetics. "Our founder Khuraira Musa". Retrieved 16 September 2019. 
  2. "The Beauty of Giving Back to Society". Africa Newspage. 16 May 2016. Retrieved 16 September 2019. 
  3. Bella Naija. "Introducing US based International Make-up Artist". Retrieved 16 September 2019. 
  4. "NGO Urges Northerners To Return Lost Glory". Daily Trust. Retrieved 16 September 2019. 
  5. "Dalilin Dana Kafa Masana'antar Kwalliya Da Shafe-Shafe". Daily Trust. Retrieved 16 September 2019. 
  6. "Arewa Groups moves to alleviate porverty". Blueprint Newspaper. 
  7. "Women for women networking". North Jersey. Retrieved 16 September 2019. 
  8. "Beauty of Entrpreneurship and the Joy of Giving Back". Blueprint Nigeria. 
Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.

Hanyoyi na waje

The contents of this page are sourced from Wikipedia article. The contents are available under the CC BY-SA 4.0 license.
Lists
Khuraira Musa is in following lists
comments so far.
Comments
From our partners
Sponsored
Credits
References and sources
Khuraira Musa
arrow-left arrow-right instagram whatsapp myspace quora soundcloud spotify tumblr vk website youtube pandora tunein iheart itunes