Jamaluddin Al-Jailani
Quick Facts
Biography
Jamaluddin Falih Al-Kilani
Shekarar haihuwa: 1972
Kasa: Iraki
Addini: Musulunci
Sana'a: Malamin jami'a, masanin tarihi, marubuci
Tasirantuwa: ya tasirantu da: Shehu Abdulkadir Al-Kilani, Imadu Abdussalam Ra'uf, Mustapha Jawad
RAYIWARSA:
Jamaluddin Falih Al-Kilani kwararren marubuci ne, mai bincike, malami masanin tarihi da hanyoyin ci gaba na al'ummar musulmai. Yana da kulawa ta musamman akan tarihin Shehu Abdulkadir Al-Kilani da abubuwan da suka shafi makarantarsa ta Kadiriyya a tsahon zamani. Tun yana yaro, karatun tarihi shi ne babban abin kaunarsa.
An haifi Dr Jamaluddin Al-Kilani a karamar hukumar Dayali dake kasar Iraki a shekara ta 1972. Jamaluddin Al-Kilani sharifi ne jikan Shehu Abdulkadir Al-Kilani kuma jikan Sayyid Hassan dan Imam Aliyyu (karramallahu wajhahu) dan Nana Fadtimah (alaihassalam).
ILMINSA
Dr Jamaluddin Al-Kilani ya yi makarantun firamare da sakandire a garin 'khadaul khalis' wanda yake a kasar Iraki; garin da yake a cike a wancan lokaci da manya-manyan masana na ilman zamani, na harshe da na addinin Musulunci. Ya samu shedar kammala digirinsa na farko a fannin Tarihi daga Jami'ar Bagadaza, kamar yadda ya samu shaidar kammala karatun difloma a wannan Jami'a a fannin harshen Turanci. Ya samu shedar digirinsa na biyu a bangaren Tarihi da ci gaban harshen Larbci da addinin Musulunci. Shedar digirinsa na uku watau PhD ya same ta ne a kan falsafar tarihin Musulunci.
Tun yana yaro, Jamaluddin Al-Kilani ya samu tarbiyya da kulawa ta musamman daga wurin mahaifinsa Dr Falih Al-Kilani, wanda mashhurin malami ne kuma marubucin rubutattun wakoki ne na adabin Larabci da addinin Musulunci a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Haka kuma ya samu kyakkyawar kulawa daga wurin babban malamin tarihi na kasar Iraki watau: Imadu Abdussalami Ra'uf.
MALAMANSA
Dr Jamaluddin Al-Kilani ya hadu da malamai da yawa wadanda ya koyi karatuttuka a wajansu da wadanda suka bashi cikakken izini na karatu, karantarwa, bincike da rubutu a fannin Tarihi da danganen kabilun Larabawa, daga cikinsu a kwai: Imadu Abdussalami Ra'uf, Salim Al-Alusi, Abdulkarim Muhammad Mudarris, Ali Al-Wardi, Abdurrazaki Al-Hasani, Muhsin Mahdi, Sa'id Abdulfattah Ashur, Muhammad Ammarah da kuma babban masani na hanyoyin jaddada koyarwar addinin Musulunci watau Majid Arsan Al-Kilani.
ILMANTARWARSA
Dr Jamaluddin Al-Kilani ya koyar a makarantun firamare da sakandire wanda daga bisani ya zamto malami mai bada karatu da horarwa a jami'ar Bagadaza, Jami'ar Mosul da ta Mustansiriyyah, kadisiyyah, Basarah, Iskandariyyah, Darul Ulum diyobandi, Jami'ar Musulunci ta Maleshiya da sauransu.
LITATTAFANSA
Dr Jamaluddin Al-Kilani ya rubuta litattafai da dama da harshen Larabci, wasu daga cikinsu an fassara su izuwa harasa daban-daban na duniya. Daga cikin litattafansa akwai:
(1) Jugrafiyyatul Bazul Ashhab - wannan littafi littafi ne da aka yi amfani da ka'idodin bincike na zamani na ilmin Tarihi domin tantance riwayun da suka yi bayanin wuri ko kasar da aka haifi Shehu Abdulkadir Al-Kilani. Tsari da abinda wannan littafi ya kunsa ya janyo hankulan masana da dama a duniya ta inda wannan littafi ya tabbatar da ingancin bayanin haihuwar Shehu Abdulkadir Al-Kilani a garin 'Jilu' dake a kasar Iraki tare da korewarsa, bisa dogaro a kan hujjoji da dama, bayanan da suke nuna haihuwar Shehun a garin Tabarustan da yake a kasar Iran. Wannan littafi ya karbu sosai-da-sosai a inda kwafi 100,000 ya kare a dan takaitaccen lokaci, abinda ya janyo maimaita buga shi har sau hudu. Muhammad Mahmud Mustapha ya fassara wannan littafin izuwa harshen Hausa.
(2) Assheikh Abdulkadir Al-Kilani: Ru'uyah Tarikhiyyah Mu'asirah - littafi ne na tarihin rayiwar Shehu Abdulkadir.
(3) Dirasatu wa Tahkiku kitab Bahjatul Asrar.
(4) Attarikul Islami: Ru'uyatun Mu'asirah - littafi ne na tarihin Musulunci a zamanance.
(5) Min As-Shakki ila Al-yakini - littafi ne da yake tabbatar da ingancin danganen Shehu Abdulkadir Al-Kilani da Annabinmu Annabi Muhammadu (salawatullahi wa salamuhu alaihi) cikakkiyar dangataka ta tsatso, bisa dogaro da hujjoji da kuma amfani da ka'idodin ilmi na zamani.
(6) Hakaza Takallamas Sheikh Abdulkadir.
(7) Tahkiku kitab Futuhul Gaib.
(8) Attarikhul Islami: Tafsirun Jadid.
(9) Al-Imamu Ahmadu Arrifa'i: Almuslihul Mujaddid.
10) Arrihlah war Rahhalah fit Tarikhil Islami.
(11) Al-Madkhal li Tarikhil Falsafatil Islamiyyah.
(12)Falsafatul Ishrak.
(13) Badi'uz Zaman Sa'idun Nursi: Kira'ah Jadidah fi Fikrihil Mustanir - littafi ne na tarihi da bayani a kan ilmin masanin Allah wanda aka yi shi a kasar Turkiyya watau Imam Annursi da bayanan nusarwa da ganarwa akan litattafansa wadanda ya rubuta su domin koya sanin Allah da hanyoyin fahimtar halittun Allah watau 'maarifa' bisa tsarin Sufanci madai-daici mai tafiya tare da zamani, domin kawo gyara da ci gaba na alkhairi ga al'ummar Annabi Muhammadu (salawatullahi wa salamuhu alaih). Littattafan Imam Annursi wadanda wannan littafi yake bayani a kansu su ne wadanda aka fi sani da 'Rasailun Nur'.
(14) Sauratur Ruh.
(15) Kurasanu Attarikhiyyah.
(16) Al-Kamusul Al-Kadiri.
(17) Al-Imamu Abdulkadir Al-Jili: Tafsirun Jadid.
LAMBOBIN YABO
Dr Jamaluddin Al-Kilani ya samu yabo saboda kokarinsa da rubuce-rubucensa daga wurin manya-manyan malamai, kungiyoyi da Jami'o'i. Farfesa Majid Arsan Al-Kilani, Fahmi Jad'an da Farfesa Imadu Abdussalami Ra'ufu sun yabi Dr Jamaluddin Al-Kilani sosai-da-sosai tare da nuna girmamawarsu ga bincikensa da rubuce-rubucensa. Haka kuma jami'o'i, kwaleji-kwaleji da kungiyoyi da dama sun bashi lambobin yabo da karramawa, daga cikinsu :
(1) IIOC - kwalejin addinin Musulunci dake London.
(2) Al-Jami'atul Islamiyyah - dake Indiya.
(3) Jami'atu Kasid Mirbah - dake Aljeriya.
(4) Al-Jami'atul Islamiyyah Al-Alamiyyah - dake Islam Abad, Fakistan.
(5) Gammayyar Kungiyoyin Musulunci dake Barazil.
(6) Al-Jami'atul Islamiyyah Al-Alamiyyah - dake Maleshiya.
(7) Jami'ar Iskandariyah.
(8) Kungiyar Gammayyar Malaman Iraki.
(9) Jami'ar Mosul.
(10) Jami'ar Ain Shams.
(11) Jami'ar Bagadaza.
(12) Jami'ar Salahuddin.
Da sauransu da yawa.