Ali Mustapha Maiduguri

Nigerian Muslim scholar
The basics

Quick Facts

IntroNigerian Muslim scholar
PlacesNigeria
wasScholar
Work fieldAcademia
Gender
Male
Religion:Islam
Birth1968
Death2019 (aged 51 years)
The details

Biography

Sheikh Dr. Ali Mustapha Maiduguri (1968-2019), Shahararren malamin addinin Musulunci ne wanda ya shafe rayuwar sa a fannin koyo da koyar da Ilimi na addinin Musulunci a Najeriya.

Farkon Rayuwar sa

An haifi Sheikh Dr. Ali Mustapha a anguwar Fezzan dake birnin Maiduguri jihar Borno Arewacin Najeriya a shekarar 1968. Mahaifin shi Alhaji Shettima Bukar Mustapha Konduga dan asalin karamar hukumar Konduga ne, mahaifiyar shi Hajiya Yakaka Bukar 'yar asalin karamar hukumar Dikwa duka a jihar ta Borno.

Tarihin karatun sa

Shi dai Dr. Ali Mustapha, ya fara karatun shi na farko a wurin mahaifin shi inda yafara da karatun Tahiya, Sallah da Al-qunutu. Daga bisami yashiga makarantar Allo (tsangaya) a wajen wani malami mai suna 'Mallam Awa' a nan unguwar Fezzan a shekarar 1972, yayi karatu har zuwa lokacin da malamin nashi ya samu larurar tabin kwakwalwa sakamakon hatsarin mota. Hakan yasa mahaifin shi yasa shi a makarantar Islamiya mai suna Madarasatul Nurul Atfan wadda a yanzu aka canja mata suna Usman Islamiya School a shekarar 1975. Bayan ya kammala Aji biyar a wancan lokacin, sai Mallam ya garzaya zuwa makarantar High Islamic Collage Maiduguri a shekarar 1982, inda yayi shekaru hudu a matakin sakandare, daganan yaci gaba da karatun Diploma a Fannin harsunan Hausa da Larabci da kuma ilimin Shari'a a wannan makarantar. Bayan ya gama a shekarar 1990, sai aka musu jarabawar daukan malamai inda yasamu nasarar zama malami a nan High Islamic college a mataki na grade ll teacher. Malam ya kwashe shekaru bakwai yana karantarwa, daganan yasamu cigaba zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina a shekarar 1997, sakamakon jinya da yayi wadda tayi sanadiyyar jinkirin zuwa, hakan yasa hukumar Makarantar ta ajiyeshi a Matakin Shu'ubah (remedial) inda yayi shekara daya daganan yasoma karatun shi a fannin Shari'a da harshen larabci anan ma malam yayi shekaru hudu. Kammalawar shi keda wuya, sai malam yanemi damar cigaba da karatun shi na digiri na biyu wato Masters degree a Fannin Uslul Fiqihi. A jarabawar da suka rubuta, malam ne yazo na daya a cikin daliban da suka zo daga Nigeria a shekarar 2002, amma bai samu damar fara karatu a wannan shekarar ba sabo da mutum biyu kacal aka dauka a cikin mutane 27 da sukaci jarabawar daga kasashe daban - daban. Daganan malam yadawo gida Nigeria inda yafara karatun babbar difiloma wato (National Diploma) a makarantar El kanemi Collage dake Maiduguri a fannain Shari'a a shekarar 2003. A shekarar 2004 kuma, malam ya garzaya Jami'ar Jos a garin Jos inda yayi karatun shi na digiri wato (Masters degree) a fannin larabci, kuma yayi nasarar kammalawa a shekarar 2006. A shekarar 2015, malam ya fara karatun digirin digirgir wato (PhD) a fannin larabci a Jami'ar Jahar Nasarawa (Nasarawa State University) inda ya kammala a shekarar 2017.

Ayyukan da matsayin da ya rike

  • Malam ya taba zama grade ll teacher a shekarar 1990 - 1997
  • Limancin Sallolin Juma'a da na Idi na tsawon shekaru 25
  • Malam yayi aiki a matsayin Daraktan shar'a a ma'aikatar harkokin addinai ta jihar Borno daga 2005 har zuwa rasuwarsa
  • A mataki na kungiya kuma, Malam shine shugaban Majalisar Malamai na farko a mataki na MMC, sannan shugaban majalisar malamai na jahar Borno.
  • Sheikh Ali Mustafa an zabe shi mamba na majalisar koli ta kasa shekaru da dama kafin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya nadashi matsayin babban Sakataren Majalisar Malamai na kungiyar Izala ta kasa bayan rasuwar Sheikh Dr. Al Hassan Sa'id Jos.

Iyali

Sheikh Ali Mustafa ya bar mata daya da 'ya'ya 15.


Manazarta

  1. https://mobile.facebook.com/JibwisNig/posts/1835000553234533
The contents of this page are sourced from Wikipedia article on 29 Feb 2020. The contents are available under the CC BY-SA 4.0 license.